Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Harbo Jirgin Saman Kasar Malaysia


 Gurgubin jirgin da aka harbo
Gurgubin jirgin da aka harbo

Ministan sufuri na Malaysia yace zai zamo mummunan laifi maras misali ga bil Adama idan har ta kasance harbo jirgin saman fasinja na kasar Malaysia a samaniyar kasar Ukraine da gangan.

Ministan sufuri Liow Tion ya fadawa 'yan jarida yau jumma'a a Kuala Lumpur cewa harbo jirgin saman fasinja da gangan ya sabawa dokoki na kasashen duniya. Yace Malaysia tana marhabin da kiran kafa hukumar bincike mai zaman kanta da zata bis awun wannan lamari inda mutane 298 suka mutu jiya alhamis.

Shugabanni a fadin duniya su na ci gaba da kiran da a gudanar da bincike dangane da faduwar wannan jirgi kirar Boeing-777 wanda ya taso daga Amsterdam a kan hanyar zuwa Kuala Lumpur. Akasarin fasinjojin dake cikinsa 'yan kasar Holland ne, kuma da yawa daga cikinsu sun doshi kasar Australiya ne domin wa ni taron duniya da za a gudanar kan cutar kanjamau ta AIDS a birnin Melbourne.

Kafofi da dama su na bayyana fargabar cewa harbo wannan jirgin saman aka yi da makami mai linzami.

XS
SM
MD
LG