Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Horas Da 'Yan Gudun Hijira Sana'oi Domin Dogaro Da Kai


Yan Gudun Hijira Dake Zaune A Cibiyar Jinya Ta Gulun Clinic Dake Jalingo
Yan Gudun Hijira Dake Zaune A Cibiyar Jinya Ta Gulun Clinic Dake Jalingo

An horas da daruruwan 'yan gudun hijira dake sansanin Minawoa sanaoin hannu.Wannan sansani dai na cikin jamhuriyar Cameroon ne.'Yan guduun hijirar zasu dogarada kansu idan sun koma garuruwan su na asali

Daruruwan ‘yan gudun hijira daga Najeriya wadanda suka bar matsugunnin su sakamakon Boko Haram suka yi tunga sasansanin ‘yan gudun hijirar dake Minawao a arewacin jamhuriyar Cameroon, yanzu suna da yiyuwar zamewa abin koyi.

Hakan ya biyo bayan horon da jamiaan MDD suka yi musu ne na zamewa mutane masu dogaro da kansu.

Zasu anfani kansu dama al’ummar su, a duk lokacin da suka koma ainihin gidajen su.

Inji wakilin wannan gidan wannan radiyon

Musali Naomi Haman wata ‘yar shekaru 29 ta kware ne ga aikin kafinta domin yawancin kujerun zama a makarantar dake cikin sansanin na Minawoa ita ce tayi su.

Naomi ta kwashe shekaru 2 cikin wannan sansanin.

Tace a cikin watan nuwabar data gabata ne ta kamala horaswan data samu na tsawon watanni 6 a matsayin kafinta.

Naomi ta zabi aikin kafinta ne sabo da idan ta koma Najeriya ya zamo cewa zata iya yin kujeru da dai wasu abubuwan anfani da kafinta zai iya yi.

Haka kuma wannan aikin hannun da ta koya yanzu ya zame mata hanyar samun kudin ta.

Wannan matar da take da ‘ya’ya biyu, tace a wani lokaci can baya ta dogara ne ga mijin ta wanda ‘yan boko haram suka kashe a Najeriya..

Tace tun daga wannan lokacin ne take dogaro da taimakon jin kai data ke samu bayan ta iso wannan sansanin a Cameroon.

Tace yanzu tana samun dala biyar bayan ta kamala yin ko wace kujera daya.

Wannan horaswan wanda ba Naomi ce kadai ta same shi ba, yana daga cikin abubuwan dogaro da kai da kwamitin kula da ‘yan gudun hijira na majilisar dinkin duniya ya samar way an gudun hijira domin su samu abin dogaro dakai ko bayan sun bar sansanin.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG