Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Inganta Matakan Tsaro A Dandalin Times Square Dake Nan Amurka


The Vienna Police

Domin kare aukuwar ayyukan taadanci, mahukunta a birnin New York dake na Amurka sunce sun inganta matakan tsaro a dandalin Times Square inda za gudanar da bikin shigowar sabuwar shekara

Hukumomi a birnin New York dake nan Amurka sunce suna kara inganta matakan tsaro a dandalin Time Square.

Hakan ko biyo bayan cewa yau ne jajibirin sabuwar shekara.

Sunyi haka ne domin kaucewa ayyukan taaddanci da aka samu birnin a cikin ‘yan kwanakin nan.

Shugabannin birnin suka ce ana sa ran mutane da yawan su yakai kusan miliyan guda ne daga sassan duniya daban-daban zasu zo wannan dandalin domin kallon bikin shigowar sabuwar shekarar 2018.

Yanzu haka dai ‘yan sandan birnin sun Makala kamarorin daukan hoto ciki da wajen haraban wannan dandalin har sama da dubu guda.

Kana ‘yan sanda da sauran jamiaan tsaro zasu yi ta sintiri a wannan wurin.

Wannan ne karo na farko da za ayi anfani da karnukan nan masu sunsuna, tare da gane mai yunkurin aikata ayyukan assha.

Don haka duk wanda zai shiga cikin wannan dandalin sai ya fuskacin tantancewa har sau biyu kafin a bari ya wure ciki ko harda wanda kare zai sunsune shi tukunna.

Sai kuma maka-makan blo da aka gindaya a wasu muhmmam wurare domin kare ayyukan ‘yan taadda.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG