Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Jinkirta Zuwa Myanmar Saboda Rashin Kyawun Yanayi


Shugabar kasar Myanmar Aung San Suu Kyi
Shugabar kasar Myanmar Aung San Suu Kyi

Duniya na kokarin kai dauki ma al'ummar Rohingya da ke shan azaba a hannun gwamnatin Myanmar, wadda ake zargi da aikata wani abu mai kama da kisan kare dangi.

An jinkirta ziyarar da wata tawagar Majalisar Dinkin Duniya za ta kai jahar Rakhine ta kasar Myanmar mai fama da tashe-tashen hankula saboda rashin kyawun yanayi.

Sanarwar dage ziyarar ta zo ne kwana guda bayan da Majalisar Dinkin Duniya ta ce wakilan na ta za su samu rakiyar jami'an gwamnatin kasar Myanmar a ziyarar da za su kai jahat ta Rakhine. Majalisar Dinkin Duniya ta ce an dage ziyarar zuwa makon gobe.

Wannan ziyarar za ta zama ta farko da wasu wakilan Majalisar za su taba kaiwa a wurin, tun bayan da Musulmin jinsin Rohingya su ka fara kaura ba ji ba gani.

Majalisar Dinlin Duniya ta fadi jiya Alhamis cewa 'yan gudun hijira sama da 500,000 su ka ketara daga kasar Myanmar zuwa kasar Bangladesh.

A halin da ake ciki kuma, mutane 13, ciki har da yara 8, sun mutu bayan da jirgin ruwan da ke dauke da su ya tintsire yayin da su ke tafiya Bangladesh daga Myanmar jiya Alhamis. An ceto 'yan Rohingya 30 daga wannan jirgin, wanda ya jidi mutane 120.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG