Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An kaddamar da Dokar ‘Yancin Marasa Lafiya A Najeriya


Mataimakin Shugaban Kasa Prof Yemi Osinbajo Ya Kaddamar Da Dokar Yancin Mararsa Lafiya
Mataimakin Shugaban Kasa Prof Yemi Osinbajo Ya Kaddamar Da Dokar Yancin Mararsa Lafiya

Mataimakin shugaban Najeriya Yemi Osinbajo ya kaddamar da dokar kare hakin marasa lafiya karon farko, da nufin kare hakkin wadanda ke cikin yanayin kunci, da kuma taimakawa marasa galihu su iya samun kula a fannin aikin jinya.

Da yake kaddamar da dokar da cibiyar sa ido da kare al’umma ta gabatar, yace za a bi tsarin sau da kafa , a kuma hukumta wadanda suka saba dokar da ake kira PBoR a takaice.

Mataimakin shugaban kasar ya bayyana cewa, ana fuskantar kalubala matuka a fannin lafiya a Najeriya sabili da haka wannan dokar zata taimaka wajen cimma gurin gwamnatin na ganin dukan ‘yan kasa sun sami kula a fannin yadda ya kamata.

Ya bayyana cewa, gwamnatin tarayya tana daukar batun kula da lafiyar al’umma da muhimmanci, dalili ke nan da yasa ta kebe kashi daya cikin dari na kudin shiga da zata samu a shekara ta dubu biyu da goma sha takwas domin kula da ayyukan jinya.

Dokar ‘yancin marasa lafiyan ta kunshi kare ‘yancin marar lafiya a muhimman fannoni goma sha biyu da suka hada da ‘yancin samun bayanan asibiti, da ‘yancin bayanin kudin jinya, da ‘yancin samun kulawa mai inganci, da ‘yancin korafi da bayyana rashin gamsuwa da yadda aka yiwa marar lafiya jinya.

Sauran fannonin da ya shafi ‘yancin marar lafiya sun hada da ‘yancin samun kulawar gaggawa, da ‘yancin kin amincewa da jinya, da kuma ‘yancin amincewa ko kin amincewa da shiga gwajin magunguna ko jinya.

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG