Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kaddamar Da Ginin Kamfanin Siminti A Nijar


Kamfanin siminti a Nijar
Kamfanin siminti a Nijar

An kaddamar da aikin gina wani katamfaren kamfanin siminti na hadin guiwa tsakanin kamfanin Dan Gwate da kuma gwamnatin Jamhuriyar Nijar, da za a gina a cikin Gundumar Keita dake jahar Tahoua.

Aikin zai lakume sefa biliyon 180, kuma, tun ranar 23 ga watan Aprilun 2014 ne shugaban kasar Nijer Alhaji Mahamadu Isuhu ya jagoranci bukin aza tubali na farko na gina wannan kamfanin.

Kafa wannan kamfanin yana da muhimmanci a yankin kasancewa zai samar da ayyukan yi da kuma kara habaka tattalin arziki cikin gaggawa. An bayyana cewa, mutane dubu biyu zasu sami ayyukan din-din-din a kamfanin simintin, yayinda wadansu mutane dubu uku zasu samun ayukan lokaci zuwa lokaci

Haka kuma ta dailin kafa wannan kamfanin simintin, kamfanin Dan Gotte zai gina makarantu, hanyoyi, rijiyoyi da samar da sauran ababan more rayuwa.

Da farko, kamfanin simintin zai rika samar da ton miliyan 1 na siminti a kowace shekara, daga bisani a kai ton miliyon 2 da rabi. Za a kuma sayar da kowanne ton a kan jikka 100 na sefa…

Binciken ya nuna cewa duk da yake an dade da fara harkokin siminti a Jamhuriyar NIjar, duk da haka kimanin kashi ishirin cikin dari ne kadai ake iya biya ta bukatar taki a kasar.

Saurari cikakken rahoton Haruna Mamman Bako:

Kafa Kamfanin siminti a Nijar-3:21"
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:21 0:00

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG