Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kaddamar da Makon Fadakarwa a kan Muhimmancin Shayar da Nonon Uwa a Nijer


Shayar Da Nonon Uwa
Shayar Da Nonon Uwa

Hukumomin kasar jamhuriyar Nijar sun kaddamar da makon fadakar da al'ummar kasar amfanin shayar da kananan yara nonon uwa, domin rage yawan mace macen kananan yara daga sabin haihuwa zuwa yan shekaru biyar a duniya

Ministan kiwon lafiyar kasar Dr Idi Mainasara ya gargadi al’ummar kasar da su bada muhimmanci ga shayar da jarirai nonon uwa tsantsansa har tsawon watanni shida. Yace wajibin mu ne mu sanar da iyaye mata da ma’aikatar kiwon lafiya da ma’aikatar kafofin yada labarai da duk masu ruwa da tsaki a wannan fanni da a jajirce wurin tallafawa sha’anin bada nonon uwa.

Wata likita a babban asibitin birnin Kwanni ta dora muryarta a kan kira ga muhimmancin shayar da nonon uwa. Tace idan aka shayar da kananan yara nonon uwa kadai har tsawon watanni shida zasu samu kariya daga cututtuka kuma zasu samu kuzari kana su shakku da iyayensu kuma su tausayawa iyayensu.

Jamhuriyar Nijer tana kebe mako guda a duk shekara domin fadakar da iyaye a kan muhimmancin shayar da kananan yara nonon uwa kadai har tsawon watannin shida da zummar kawo karshen cututtuka da mace macen yara sababbin haifuwa zuwa shekaru biyar.

please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG