Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kaddamar Da Neman Tallafi Na 'Yan Gudun Hijirar Sudan Ta Kudu


Yan gudun hijirar Sudan ta Kudu
Yan gudun hijirar Sudan ta Kudu

Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci mutane su taimakawa asusun da ta bude domin tallafawa 'yan gudun hijir Sudan ta Kudu, sama da mutane miliyan biyu da su ke neman agajin gaggawa.

Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce tana neman tallafin dala miliyan dubu biyu da miliyan dari bakwai, domin taimakawa ‘yan gudun hijirar Sudan ta Kudu sama da miliyan biyu da ke bukatar agaji.

‘Yan gudun hijirar a cewar hukumar, na zaune a wani mawuyacin hali a wasu kasashe shida, da ke makwabtaka da kasar, yayin da kudaden da ake amfani da su wajen tallafa musu ke gab da karewa.

Matsalar ‘yan gudun hijirar Sudan ta Kudu, ita ce mafi girma a Nahiyar Afirka, wacce kuma ke samun mafi kankantar kudaden tallafi.

Hukumar kula da ‘yan gudun hijirar ta bayyana cewa, kashi 38 kadai cikin 100 na yekuwar neman taimakon dala miliyan $1.4 da ta nema aka samu.

Sai dai hukumar ta bayyana cewa, zafin rikicin kasar ya kwanta, saboda yarjejeniyar zaman lafiya da aka kulla a watan Satumba, bayan da kasar ta kwashe shekaru biyar tana fama da yakin basasa.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG