Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Bayyana Shakku A Kan Yanayin Mutuwar Jakelin A Hannun jami'an Amukra


Jami'an Kan Iyakar Amurka da Mexico
Jami'an Kan Iyakar Amurka da Mexico

Mutuwar wata yarinya mai shekaru bakwai ‘yar kasar Guatemala a hannun jami’an tsaron kan iyakar kudu maso yammacin Amurka a makon da ya gabata, ta dora ayar tambaya a kan yanda jami’an tsaron iyakar suka yiwa batun rashin lafiyar yarinyar rikon sakainar kashi.

Wannan lamari dai ya haddasa jinkirin wurin sanar da mutuwar yarinyar ga jama’a da kafofin yada labarai da ma majalisun tarayya.

Bincike a kan mutuwar Jakelin Caal Maguin ya kara girma a jiya Juma’a, inda sufeto janar na ma’aikatar tsaron cikin gida yake cewa zasu duba yanda ma’aikatar kostom dake kula da harkokin kan iyakar suka riki batun rashin lafiyarta a lokacin da ta kwashe sa’o’I 27 tana hannunsu har izuwa lokain da ta mutu.

Jakelin ta tsallako kan iyaka ta shigo Amurka tare da mahaifiyarta mai shekaru 29 Nery Caal Raxruha a yankin Alta Verapaz a arewacin Guatemala.

Ma’aikatar kostom Amurka ta tsare yarinyar da mahaifiyarta ne da yammacin ranar shida ga watan Disamba a cikin gungun mutane 163 da suka tsallako ta wata barauniyar hanya dake kauyen kudancin New Mexico wanda ke kusa da iyakar Antelope Wells a cewar ma’aikatar kostom. Sun ce binciken farkon da suka gudanar a kan yarinyar bai nuna akwai wata damuwa ba.

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG