Accessibility links

An Kaddamar Da Rigakafin Shan Inna Karo Na Biyar A Jihar Naija

  • Grace Alheri Abdu

Wani wanda cutar shan inna ta gurguntar yana jawabi wajen wani taro
An kaddamar da Rigakafin yaki da ciwon shan inna karo na biyar a jihar Minna, Najeriya.

A cikin jawabinsa wajen kaddamar da rigakafin da aka gudanar a garin Tagina dake yankin masarautar Kagara, wakilin Hukumar Lafiya ta duniya, Mr. Bolaji Buhari ya bayyana cewa, kananan yara ishirin da biyar ne suke dauke da cutar a Najeriya a halin yanzu.

Wakilinmu Mustapha Nasiru Batsari da ya halarci bukin, ya ruwaito cewa, yau Jumma’a ne za a ci gaba da aikin rigakafin, har ya zuwa talata sha takwas ga wannan wata.

XS
SM
MD
LG