Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kaddamar Da Shirin Sauyin Yanayi a Nijar


Wata yarinya na tafiya a gefen hanya da aka tara yayin kara bayan girbi
Wata yarinya na tafiya a gefen hanya da aka tara yayin kara bayan girbi

Hukumar Amurka mai kula da raya kasashe domin samar da ci gaba ta USAID tare da hadin gwiwar hukumar binciken sararin samaniya NASA sun kaddamar da wani shiri na musamman da ake kira SERVIR.

An kaddamar da shirin ne a cibiyar bincike da bunkasa harakokin noma da albarkatun ruwa da kimiyar yanayi dake Jamhuriyar Nijar.

Shirin zai samar da bayanan da za su taimakawa kasashen yankin Afrika ta yamma su tunkari matsalolin dake da nasaba da canjin yanayi.

Matsalar sauyin yanayi ya fi iya shafar kasashe masu tasowa, saboda karancin matakai da ake zargin hukumomi ba sa dauka.

Kasashen yankin Sahel ne suka nemi Amurka da ta tallafa musu da matakan kariya ga sauyin yanayi.

Domin jin cikakken bayani kan wannan batu, saurari rahoton Sule Mumuni Barma daga Yamai:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG