Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kaddamar Da Yakin Takarar Shugaban kasa A Burundi


Ana shirin kaddamar da takarar neman zaben shugaban kasar Burundi yayin da hukumomi ke fatan Allah zai kare al’umma daga kamuwa da cutar coronavirus, wanda a yanzu haka mutune 15 ne ke dauke da ita, kuma daya ya mutu a kasar da ke tsakiyar Afika.

'Yan takara 7 ne suka kaddamar da gangamin neman zabe, tare da tarukan mutane masu yawa, duk da cewa wasu gwamnatocin Afrika na kira da a nisanci taro mai yawan jama’a don hana yaduwar cutar coronavirus.

Ranar 20 ga watan Mayu ake sa ran gudanar da zabukan shugaban kasa, 'yan majalisu, da na kananan hukumomi a kasar.

Shugabannin jam'iyun adawar kasar na zargin shugaba Pierre Nkurunziza da nuna halin ko-in -kula ga rayukan jama’a da kin daga zaben

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG