Accessibility links

An Kaddamar da Shimfida Layin Dogo Wa Kasashe Biyar


Mahamadou Issoufou shugaban Jamhuriyar Niger

An kaddamarda bikin shimfida layin dogo a jamhuriyar Niger wanda zai taso daga kasar Binin zuwa Niger ya wuce har zuwa kasar Kamaru.

Jiya aka yi wani gagarumin bikin shimfida layin dogo a jamhuriyar Niger wanda yana cikin alkawarin da shugaba Yousouf Manmadou ya yiwa al'ummar kasar can baya.

An kafa tubalin layin dogon a birnin Niamey. Wanda zai taso daga jamhuriyar Binin zai hadu da na Niger ya wuce wasu kasashe. Layin dogon zai ratsa garuruwan Gaya da wasu kana ya isa Niamey. Aikin da aka fara jiya zai kwashi watanni ashirin ana yi kana zai ci kudi sama da miliya dari bakwai na sefa.

Layin dogon zai kai nisan samada kilomita dubu daya. Zai ratsa tsakanin kasashen Binin da Niger da Togo da Burkina Faso ya wuce zuwa kasar Ivory Coast,kafin ya tsatya a kasar Kamaru.

A cewar shugaban kasar Niger Mahamadou Issoufou da ya jagorancin bikin yace layin dogon kyauta ne ga kasarsa a yayin da yake cika shekaru uku da rike madafin ikon kasar. Yace bikin zai shiga tarihi. Abu ne da ba'a taba gani ba. An jima ana jiranshi amma sai gashi Allah Ya nuna wa al'ummar kasar. Yace abun farin ciki ne ga gwamnati da 'yan kasa duka.

Kamfanin Faransa da ake kira Bolori shi ne zai gudanar da aikin kuma tuni ya kawo taragu biyu ya ajiye abun da ya nuna za'a fara aikin gadan gadan.

'Yan kasar da aka zanta da su sun fadi albarkacin bakinsu. Wani cewa yayi yana jin za'a yi layin dogo amma bai taba jin hakan zai faru ba sai lokacin shugaba Mahamadou Issoufou. Wani Rabiu Abdulrahaman ya yiwa Allah godiya da ya ga ranar. Yace abu ne da suke gani a kasashen waje sai gashi Allah Ya kawo masu. Yace ya ji dadi sosai domin wannan ya fi karfin zancen teburin mai shayi. Wata Hajiya tace ta ji dadi ta kuma godewa Allah. Tace ko ta mutu jiyan ta godewa Allah tun da ta ga taragun da aka kawo.

Ga rahoton Abdullahi Mamman Ahmadu.
XS
SM
MD
LG