Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kafa Asusun Taimakawa Kasashen dake Fama da Gurbacewar Yanayi


Shugaban Najeriya Muhammad Buhari

A taron kasa da kasa kan canjin yanayi shugaban Najeriya Muhammad Buhari ya bayyana irin illar da gurbacewar yanayi yake yiwa kasashe masu tasowa saboda masana'antun manyan kasashen duniya lamarin da ya sa taron ya kafa asusun taimakawa kasashen dake fama da gurbacewa yanayi.

Ministan muhallin Najeriya Alhaji Ibrahim Jibrin Wamban Nasarawa ya bayyana irin ribar da kasashe kanana da masu tasowa kamar Najeriya suka ci a taron.

Yace babban ribar da kasashen suka samu shi ne amincewa da kafa wani asusu da za'a dinga anfani dashi ana tallafawa kasashe masu bukata kamar Najeriya. Kasashe irinsu Najeriya ba su ne suke sarafa abubuwan dake kawo gurbatar muhalli ainun ba amma sun fi kowa shan wuya, inji Alhaji Jibrin.

A cewar Alhaji Jibrin shugaban Najeriya Muhammad Buhari yayi magana mai sosa rai tare da bada misali da tafkin Chadi wanda yake kafewa kowace shekara saboda gurbatar yanayi.

Ministan ruwan Najeriya Injiniya Huseini Adamu wanda shi ma ya halarci taron yace tafkin Chadi na samun ruwa ne daga ruwan sama amma canjin yanayi ya sa tafkin na bushewa domin ruwan sama ya ragu. Yace haka ma zafin rana dake kwararowa daga hamada yana sa tafkin ya bushe. Inji Injiniya Adamu idan aka cigaba a haka watarana tafkin zai bushe gaba daya.

Ga rahoton Hassan Maina Kaina da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:15 0:00

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG