Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kafa Dakarun Soji Na Musamman da Zasu Shawo Kan Sabon Salon Boko Haram


Sojoji Na Musamman
Sojoji Na Musamman

Rundunar sojojin Najeriya ta kafa dakaru na musamman wadanda aka basu kayan yaki na zamani da zasu shawo kan sabon salon kai hare hare da kungiyar Boko Haram ta fito dashi ta hanyar kai harin sari ka noke tare da bin sawun 'yan ta'addan duk inda aka ji labarinsu

Dakarun da aka samar masu kayan YAKI irin na zamani zasu shawo kan yadda Boko Haram ta fito da sabon salon yiwa sojoji kwantan bauna da kuma kai farmaki kan motocin dake tafiya bisa tituna a shiyar arewa maso gabashin Najeriya.

Dakaru na musamman suna horo
Dakaru na musamman suna horo

Kakakin hedkwatar sojin kasar Birgediya Janar Sani Usman Kukasheka ya yi karin bayani. Yana mai cewa dakarun sojojin 'yan kada ta kwana ne kuma ba zasu kasance wuri guda ba. Kodayaushe suna kan tafiya suna kutsawa wurare. An rabasu rukuni rukuni domin su dinga shiga lungunan da 'yan ta'addan suke samun mafaka.

Matasan yankin irinsu Alhaji Adamu Yaro Potiskum sun fara nuna kwarin gwuiwa akan wannan sabuwar dabarar.

Dr. Useni Hassan wani kwararre yace yana da kyau a hada da neman goyon bayan mazauna yankunan karkara musamman na yankin da 'yan ta'addan suke. Yace a saka mutanen cikin wannan sabon shirin kamar basu lambar wayar sojoji da zasu tuntuba da zara sun ga wani mugu.

Ga rahoton Hassan Maina Kaina da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:31 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG