Accessibility links

An Sake Kafa Dokar Hana Fita Na Sa'o'i 24 A Duk Fadin Jihar Kaduna.

  • Aliyu Imam

Wasu wuraren ibada da aka kai wa hari a karshen mako.

Sakamakon barkewar sabon rikici a Kaduna da kewaye, gwamnatin jihar ta kafa dokar hana fita a duk fadin jihar.

Sakamakon barkewar sabon rikici a safiyar Talata bayan da gwamnatin jihar Kaduna ta sassauta dokar hana fita da ta yi ranar litinin, hukumomin jihar sun sake maido da dokar hana fita na sa'o'i 24 a duk fadin jihar.

Kwamishinan yada labarai na jihar Kaduna Sa'idu Adamu ne ya bayyana haka a hira da sashen Hausa na Muriyar Amurka yayi da shi. Kwamishinan yace, an wayi gari lafiya, har mutane sun tafi bakin aiki, 'yan kasuwa sun kama sana'a, sai kurum matasa daga banagaren musulmi da kirista a sassa da suka fi karfi suka fara kone konen tayoyi.

Daga nan kuma wasu suka shiga fasa kantuna suna diban ganima. Wasu suna kona gine gine da wuraren ibada daban daban. Kamar yadda zaku ji cikin wan nan hira da Kwamishinan yada labarai na jihar.

Ra’ayinka

Show comments

XS
SM
MD
LG