Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kafa Dokar Hana Fita a Garin Ibi


Gwamnan Jihar Taraba, Danbaba Suntai

Hukumomin tsaron a jiharTaraba sun tabbatar da adadin wadanda aka kashe

Biyo bayan wani sabon rikici a garin Ibi dake kudanshin jihar Taraba, yanzu an kafa dokar hana fita har sai illamasha Allahu.

Hukumomin tsaron a jihar sun tabbatar da adadin wadanda aka kashe ya karu, da yake tabbatar da karuwar kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Joseph Kwaje, yace fararen hula goma sha biyu da Sojoji biyu aka kashe.

Ya kuma kara da cewa an kuma kama mutane goma sha hudu da kuma makamai.

Cikin kwanakinan dai yankin Ibi dama Wukarin dake kudancin jihar Taraba na ta fama da tashe- tashe hankula da so tari yake komawa fadan kabilanci dana addini, wanda yasa wasu masauna gari yin gudun hijira.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:21 0:00
Shiga Kai Tsaye


XS
SM
MD
LG