Accessibility links

Shugaba Goodluck Jonathan yace kafa dokar-ta-baci a jihohin Borno da Yobe da kuma Adamawa zai taimaka wajen kare rayukan al'ummar wannan yanki

Shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya ya ayyana kafa dokar-ta-baci a jihohin Adamawa, Borno da kuma Yobe, domin shawo kan matsalolin tsaron da yace sun wuce gona da iri a wadannan jihohin.

A cikin jawabin da yayi da maraicen Talata ga al'ummar Najeriya, shugaban na Jam'iyyar PDP yace a matsayinta na hukumar da al'umma suka damkawa hakkin kare kasa, ala tilas gwamnati ta dauki wannan matakin domin shawo kan abinda ya kira "'yan ta'addar da suka addabi jama'a" a wadannan yankunan.

Shugaban yayi tur da tashe-tashen hankulan dake faruwa a kasar da kuma masu haddasa su.

Wakilin Muryar Amurka, Nasiru Adamu El-Hikaya ya ji ta bakin masanin harkokin siyasa, kuma malami a jami'ar Abuja, Buhari Bello Jega, wanda yace Gwamna bashi da aiki, idan bashi da iko akan batun tsaro a jiharsa. A cewarshi, Gwamna "Fanko" ne idan aka ce ya zauna akan kujerar shugabanci, duk da cewa an kafa dokar ta baci a jihar da yake jagoranta.

Shi ko Ado Adamu Bon-boi, wanda shugaba ne na matasan PDP a karamar hukumar Gujuba cewa yayi "Gwamnati tayi dai-dai" da ta kafa wannan doka, wanda ke nufin za'a kara adadin sojoji a wadannan jihohi.

Ra’ayinka

Show comments

XS
SM
MD
LG