Sudan ta Kudu ta bude wani sabon babi a yau Asabar, bayan da bangarorin da ke hammaya da juna suka kafa gwamnatin hadin kai, matakin da masu lura da al’amura da dama ke fatan ya dore.
Kwana guda bayan da Shugaba Salva Kiir ya rusa gwamnatinsa, an rantsar da shugaban ‘yan adawa Riek Machar a matsayin mataimakinsa, tsarin da har sau biyu ana bi amma yake rugujewa.
Bangarorin biyu sun sha tafka fada, wanda ya zuwa yanzu ya yi sanadiyyar mutuwar mutum kusan dubu 400.
A shekarar 2013, Sudan ta Kudu kasar da ita ce ‘yar autar a duniya, ta fantsama cikin yakin basasar da magoya bayan Kiir da Machar suka yi ta gwabza fada, shekara biyu bayan fafutukar da ta yi ta yi, ta neman ‘yancin kai daga Sudan.
Kasashen duniya da dama sun yi ta shiga tsakani don ganin an sasanta rikicin, inda har a bara shugaban mabiya darikar Katolika Paparoma Francis, ya durkusa ya sumbaci kafafun Kiir da Machar, a matsayin yana rokon su yi sulhi na dindindin, wani abu da ba taba ganin ya yi ba.