Accessibility links

An Kafa Kwamitin Zaman Lafiya a Jihar Taraba


Mutane suka hallara a wurin da aka kai hari

A wani kokarin kawo karshen kashe-kashe tsakanin kabilun Tiv da Jukun da Fulani gwamnatin jihar Taraba ta kafa kwamitin zaman lafiya

Mukaddashin gwamnan jihar Taraba ya jagoranci taron sulhu tsakanin Fulani da Jukun da kabilar Tiv har da ma hausawa.

Taron sulhun ya samu halartar shugabannin kananan hukumomin da suka fada cikin rigingimu da sarakunan gargajiya da shugabannin siyasa.

A jawabin bayan taron wanda shugabannin Miyatti Allah da na Tiv da Jukun suka amince da shi sun yi gargadin a daina kaiwa juna hari a yafewa juna domin a zauna lafiya. Dan majalisa Daniel Gani daya daga cikin 'yan siyasar kudancin jihar dake kan gaba wurin neman an sasanta yace su mutanen Wukari sun kafa kwamiti su tantance yadda zasu fitowa al'amarin. Yace idan ma Fulanin yankinsu ne ke da damuwa su fito a zauna a daidaita. Idan kuma ba Fulanin wurinsu ba ne a tantance damuwarsu. Yace ana kashe juna har ma ta kaiga daukan ran yayansa.

Mukaddashin gwamnan jihar Alhaji Garba Umaru ya nemi shugabannin yankin su kai zuciya nesa domin a samu zaman lafiya. Yace yau sun zauna an kafa kwamiti na zaman lafiya. Kabilar Tiv da Fulani sun tabbatar masu ba zasu cigaba da fada ba. Idan aka cigaba da fitina ita gwamnati ma ba zata iya taimakawa mutane ba har su samu cigaba. Yayi fatan wannan abun dake faruwa ya zama na karshe.

Ga rahoto.
XS
SM
MD
LG