Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An kai hare hare akan coci coci guda uku a jihar Kaduna

Irin barnar da ake hadasawa, a sakamako hare haren da ake kaiwa Nigeria ke nan

Bama bamai sun tashi a coci guda uku a jihar Kaduna arewacin Nigeria. Hukumomin Nigeria sun baiyana an kai hare hare a coci guda biyu a birnin Zaria, a yayinda aka kai hari akan coci na uku a Kaduna.

Bama bamai sun tashi a coci guda uku a jihar Kaduna arewacin Nigeria. Hukumomin Nigeria sun baiyana an kai hare hare a coci guda biyu a birnin Zaria, a yayinda aka kai hari akan coci na uku a Kaduna.

Shedun gani da ido su fadawa Muryar Amirka cewa, daruruwan mutane ne suka yi bore bayan harin na Kaduna, amma nan da nan yan sanda suka murkushe bore.

Haka kuma, shedu gani da io sunce tashin bama bamai sun jikatta mutane to amma nan da nan ba’a san yawan wadanda suka jikkata ba.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG