An yi ta kai hare-haren sama akan Tripoli, babban birnin Libya, yayin da dakarun da ke marawa Janar Khalifa Haftar, da abokanan hamayyarsu na bangaren gwamnatin ke ci gaba da artabu a daren jiya Asabar.
Wakiliyar Muryar Amurka, Heather Murdock wacce ke birnin na Tripoli, ta ruwaito cewa, hare-haren, sun fi maida hankali ne kan wani yanki da ke kusa da filin tashin jiragen birnin.
Ta kara da cewa, an ji tashin jirage marasa matuka a lokacin da wasu fashe-fashe guda hudu zuwa shida suka auku.
Wasu rahotanni da ba a tabbatar ba, sun bayyana cewa mutum guda ya mutu, yayin da mutane da dama suka yi ta wallafa hotunan bidiyo a shafukan sada zumunta, wadanda suka nuna lokacin da aka kai hare-haren da jirage mara matuka.
Su dai dakarun da ke marawa Khalifa Haftar baya, na kokari ne su karbe ikon birnin na Tripoli daga hannun Firai Minista Fayez Al Sarraj, wanda kasashen duniya suka amince da gwamnatinsa.
Tun da suka kaddamar da hare-harensu a farkon watan Afrilu, birnin na Tripoli ya yi ta fama da haren-haren sama, wadanda ake kyautata tsammanin da jirage mara matuka ake kai su.
Wannan fada tsakanin bangarorin biyu, ya saka rayuwar mazauna kusa da birnin cikin hadarin gaske.
Facebook Forum