Ofishin Jakadancin Amurka a Saudiyya yana gargadi ga Amurkawa suyi takatsan tsan a yankin da kuma ciki da kewayen fadar da ake kira ta lumana, bayan rahotanni an kai hari a wurin dake birnin Jeddah
Ma'aikatar harkokin cikin gidan Saudiyya ta fada yau Asabar ceewa, an kashe wasu masu gadin 'yan kasar biyu, wasu uku sun jikkata sakamakon harin da wani mutum cikin mota, wand a yazo wurin kuma ya bude wuta.
Kakakin ma'aikatar yace masu tsaron fadar sun harbe suka kashe maharin.
Kakakin yace maharin wani dan kasar ne dan shekaru 28 da haifuwa mai suna Mansour al-Amri.
Facebook Forum