Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kai Hari Kasar Kamaru


Sojojin shiyya ta 7 dake Maiduguri sun gano inda harhada bam a Kumshe

Rahotanni daga kasar Kamaru na nuni da cewa wadansu mahara da ake kyautata zaton ‘yan kungiyar Boko Haram ne sun kai hari a kauyen Guraya dake karamar hukumar Maraya dake jihar Arewa Mai Nisa ta kasar Kamaru dake kan iyaka da Najeriya.

Harin da aka kai da misalin karfe daya na daren jiya Jumma’a ya yi sanadin asarar rayuka da dama da kaddarori.

Shaidun gani da ido sun shaidawa Sashen Hausa na Muryar Amurka cewa, maharani sun dauke sa’oi hudu suna kai hare hare da kone kone kafin jami’an tsaro suka kawo dauki sai dai kafin su iso maharan sun kona galibin gine ginen dake garin.

Mutumin da Wakilin Sashen Hausa ya yi hira dashi ya bayyana cewa, harin da aka kawo a daidai lokacin da ake gudanar da taron harkokin tsaro, manuniya ce cewa kungiyar tana so a san har yanzu tana da karfin kai hare hare.

Ga cikakken rahoton da wakilinmu Awal Garba ya aiko mana daga kasar Kamaru

Rahoton hari a Kamaru-2:2"
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:12 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG