Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kai Hari A wani Coci Dake Quetta A Kasar Pakistan


This photo released by Vicenza Diocese, Saturday April 5, 2014 shows Vicenza Bishop Beniamino Pizziol, center, flanked by father Gianantonio Alllegri, right, and Giampaolo Marta, left, during a mass in Tchakidjebe church, near Maroua, Cameroon, during a
This photo released by Vicenza Diocese, Saturday April 5, 2014 shows Vicenza Bishop Beniamino Pizziol, center, flanked by father Gianantonio Alllegri, right, and Giampaolo Marta, left, during a mass in Tchakidjebe church, near Maroua, Cameroon, during a

Wasu yan taadda sun kai wa wani wurin ibadan kirista hari har suka kashe mutane 8 kana wasu da dama suka samu rauni

Wasu mutane ukku dauke da bindigogi wadanda kuma ‘yan kunar bakin wake ne sun afkawa wani cocin dake da cincirondon mutane dake gefen garin kudu maso yammacin birnin Quetta na kasar Pakistan kuma sun kashe mutane 8.

Jamiain gwamnati da likitoci sunce mata da yara na cikin wadanda wannan balain ya rutsa dasu, a cocin da ake kira Bethel Memorial Church.

Shedun gani da ido sunce wadannan maharan sunyi kokarin shiga ainihin babban dakin dake dauke da mutane sama da 400 inda masu ibadar ke gudanar da ibadar su a yau lahadi amma ‘yan sanda dake gadin bakin kofar suka hana su, har ma suka kashe daya daga cikin su, shi kuma na biyun sai ya tada bomb din dake jikin sa a wajen cocin.

‘Yan sanda suka ce wannan bomb din ya jima wani mai gadi mummunar rauni.

Babban jamiin ‘yan sandan lardin Sufeta Janar Moazzam Ansari ya fada wa manema labarai cewa mutun na ukku daga cikin maharan ya tsere zuwa wani gida kusa da cocin lokacin da akayi musayar wuta dasu, yace amma ana nan ana kokarin ganin an kama shi.

Ansari yace da mutanen da zau mutu ALLAH kadai yasan iyakar su ba don ‘ya sanda dake gadin bakin kofar shiga cocin ba da suka yi saurtin gane su kuma suka bude musu wuta.

Quetta dai inda wannan abin ya faru nan ne babban birnin Baluchistan inda kai hare yayi Kamari cikin ‘yan kwanakin nan.

Sai dai kawo yanzu ba wanda ya dauki alhakin aikata wannan danyen aiki.

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG