Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An kai Hari a Wata Makarantar Sakandaren Garin Potiskum


Wani likita a Asibitin Gwamnati dake Potiskum na kula da wani dalibin Makarantar Sakandanran Gwamnati ta Mamudo.

Rayuka sun salwanta, wasu da dama kuma sun raunata sanadiyar fashewar wani Bom a garin Potiskum,

Wani dan kunar bakin wake ya tada bom a wata makarantar sakandare dake garin Potiskum na jihar Yobe a yau dinnan, wanda yai sanadiyar hasarar rayuka da kuma jikkata wasu da dama.

Muryar Amurka tayi hira da wani malamin makarantar wanda ya so a sakaya sunansa, malamin yace harin ya faru da safiyar yau ne, Yayinda daliban makarantar gwamnati da ke garin Potikum ke jiran jawabin shugaban makarantar. Kafin fara jawabin shugaban ne wani sanye da kayan makaranta, goye da jakka a baya ya fasa Bom din, shima maharin ya hallaka sanadiyar harin iji malamin.

“Wannan shine karo na ukku da aka yi kokarin kai hari a makarantar amma na yau ne kawai ya tashi” a ta bakin malamin. Sai dai a lokacin, malamin bai iya bada adadin wadanda suka rasa rayukansu ba ko kuma suka jikkata sanadiyar harin.

ga hirar da Ibrahim Alpha Ahmed yayi da Malamin

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:18 0:00
Shiga Kai Tsaye

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG