Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kai Hari a Yankin Ngalewa Dake Jamhuriyar Nijar


Gawarwaki dake rubewa a garin Damasak da aka kwato kwana kwanan nan, Maris 20, 2015

A karo na biyu cikin mako guda wasu mahara sun kai hari a yankin Ngalewa dake Jamhuriyar Nijar, inda ake kyautata zaton cewa maharan 'yan kungiyar Boko Haram ne, inda akalla mutane tara suka mutu.

Wasu da ake zaton 'yan Kungiyar Boko Haram ne sun kai hari a garin Ngalewa mai tazarar kimamnin kilomita 100 da birnin Diffa a Jamhuriyar Nijar.

A wannan harin, 'yan ta’addan sun kashe mutane tara kana suka yi awon gaba da mata da yara da kuma matasa da dama zuwa wani wurin da ba a sani ba.

Rahotanni sun ce gwanman jihar Diffa ya kai ziyara garin na Ngalewa don halartar jana’izar wadanda suka mutu a wannan harin kana jami’an tsaro sun fara farautar 'yan ta’addan don su kwato wadanda suka yi awon gaba dasu da kuma mayar da martani kan wannan hari.

Ya zuwa yanzu hukumomin kasar ba su fidda wata sanarwa a kan wannan mummunan harin a hukumance ba, kazalika, yunkurin da wakilin sashen Hausa ya yi na tuntubar jami’an gwamnatin kasar a lokacin hada wannan rahoto don jin ta bakinsu game da wannan hari ya cutura.

Saurari wannan rahoto domin jin karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:50 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG