Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kai Hari Kan Filin Jirgin Saman Da Amurka Ke Amfani Da Shi A Somaliya


Wasu mayakan kungiyar Al Shabab
Wasu mayakan kungiyar Al Shabab

Mayakan Al-Shabab sun kaddamar da hari kan wani filin tashin jirage da sojojin Amurkan suke amfani da shi wajen taimakawa dakarun Somaliya, in ji wasu majiyoyin tsaro.

Mayakan sun tayar da abubuwa masu fashewa ne daga wasu manyan motoci guda biyu a tashar jirgin saman Ballidogle, da ke yankin Shabelle ta kudu, kusan kilomita 90, yamma da Mogadishu.

Wata majiya daga yankin ta ruwaito jin fashewar abubuwa biyu a kusa da filin jirgin saman.

Bayan kai harin, kungiyar Al Shabab ta fito ta dauki alhakin kai sa, yayin da wata sanarwa daga dakarun Amurka ta ce babu wani sojanta ko na Somaliya da ya ji rauni.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG