Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Har Yanzu Ana Kashe Mutane a Hanyar Birnin Gwari


Janar Lucky Irabor (Facebook/Nigeria Defense)
Janar Lucky Irabor (Facebook/Nigeria Defense)

Duk da kokarin da gwamnatin jahar Kaduna ke cewa ta na yi don magance matsalar tsaro, al'ummar yankin Birnin Gwari sun ce hare-haren 'yan-bindiga a yankunan su na kara kamari domin sun fara afka wa sujojin dake rakiya ga motoci.

Dama dai tafiya a hanyar Birnin Gwari zuwa Kaduna sai da jami'an tsaro ake yin ta, ta yadda idan an tara motocin da za su Kaduna ko Birnin Gwari sai motar sojoji daya ta wuce gaba daya kuma na baya. Sai dai kuma 'yan-bindigan da ke dajin Birnin Gwarin sun fara afka wa tawagar motochin da jami'an tsaron da ke tare da su, inji wani dan yankin na Birnin Gwari.

Masani kan harkokin tsaro Dakta Yahuza Ahmed Getso dai na ganin matsawar ba a tashi tsaye ba, matsalar hare-haren 'yan-bindiga za tura mutane bango.

Kokarin jin ta bakin rundunar sojan Najeriya da ke Kaduna gameda wannan farmaki ya ci tura sai dai kuma kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jahar Kaduna, Malam Samuel Aruwan ya sha nunar da kokarin da jami'an tsaro ke yi wajen murkushe 'yan-bindiga a fadin jahar Kaduna.

Duk da saukin hare-haren 'yan-bindiga da ake ganin an samu a wasu sassan jahar Kaduna dai, 'yan-bindigan sun tare hanyar Kaduna-zuwa Abuja a ranakun Lahadi da Litinin, duka da yamma, sai kuma ga shi sun tare hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari kashe gari.

Saurari rahoton Isah Lawal Ikara:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:28 0:00


XS
SM
MD
LG