Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kai Harin Bindiga Har An Kashe Wata Mata a Jihar Texas


'Yan Sanda a Wajen Da Aka Yi Harbin Birnin Austin Da Ke Jihar Texas

Jami’ai a jihar Texas da ke nan Amurka sun bada bayanin cewa an sami wasu harbe-harbe har kashi biyu a babban birnin kudancin jihar.

Kafafen yada labaran cikin gida sun bada rahotannin wadannan harbe-harben, tare da cewa har an kashe mace daya da jikkata wasu a birnin na Austin.

‘yan sanda sun ce sun mamaye yankin da aka yi harbin, sannan sun gargadi mutane da su killace kansu daga kusantar inda abin ya faru.

Tuni dai jami’an ‘yan sandan Amurka suka zama a ankare irin wadannan hare-hare, biyo bayan harin da aka kaiwa ‘yan sanda a Dallas.

A lokacin zanga-zangar yin tir da kisan gillar da jami’an tsaron ke yiwa jama’a musamman ma bakaken fata. Sanadiyyar zanga-zangar ne wani bakar fata ya bindige ‘yan sanda biyar a birnin.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG