Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kai Tagwayen Hare Hare Da Gurneti A Kenya


Wata mace 'yar Ingila da akayi garkuwa da ita a Somalia, ake rakata ta shiga jirgi, bayan an sakota.

An kai wasu kusan tagwayen hare hare da gurneti a birnin Mombasa na Kenya dake kan gabar teku da kuma wani kauye kusa da birnin a yammacin jiya Asabar, mutum daya ya ras ransa wasu akalla 24 kuma suka jikkata.

An kai wasu kusan tagwayen hare hare da gurneti a birnin Mombasa na Kenya dake kan gabar teku da kuma wani kauye kusa da birnin a yammacin jiya Asabar, mutum daya ya ras ransa wasu akalla 24 kuma suka jikkata.

Jami’ai suka ce wasu mahara da ba’a san ko su wanene bane sun jefa gurneti a wani taron mabiya addinin kirista a kauyen Mtwapa dake arewacin Mombasa, har mace daya ta rasa ranta da raunata fiyeda mutane 10.

A Mombasa kuma an kai harin gurneti na biyu kan wani wurin cin abinci dake kusa da babban dandalin wasanni. Nan kuma akwai rahotanni dake cewa an raunata mutane da dama.

Kenya ta fuskanci harin sari ka noke da gurneti a babban birnin kasar Nairobi, bayan da kasar ta kutsa a makwabciyarta Somalia cikin watan oktoban bara, da nufin yakar tsagerun kungiyar al-shabab masu da’awar islama. Amma wan nan ne karo na farko da aka kai hari a Mombasa, birni dake da farin jinni ga ‘yan yawon bude ido.

Gwamnatin kenya tana zargin kungyar al-shabab mai alaka da al-Qaida da laifin kai hari da satar ‘yan yawon bude ido cikin kasarta. Amma al-shabab ta musanta cewa tana da hanu a hare haren gurneti da aka kai cikin Kenya a baya bayan nan.

XS
SM
MD
LG