Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kai wa Shingen Binciken Motoci Harin Kunar Bakin Wake a Masar


Yadda hayaki ya turnike sararin samaniya a wani hari da aka kai a Masar
Yadda hayaki ya turnike sararin samaniya a wani hari da aka kai a Masar

Wani harin kunar bakin wake da aka kai kusa da garin Rafah a kasar Masar ya yi sanadiyar rayukan sojoji goma.

Jami’ai a kasar Masar sun ce wani harin kunar bakin wake da aka kai da mota a shingen binciken motoci a Arewacin Sinai, ya kashe sojoji 10.

Har yanzu dai babu wani ko wata kungiya da ta fito ta dauki alhakin kai harin kusa da garin Rafah a yau Juma’a.

Masar dai na fama da hare-haren ta’addanci tun shekarar 2013, lokacin da sojoji suka hambare gwamnatin shugaba Mohamed Morsi, bayan wata gagarumar zanga-zanga.

A daya bangaren kuma, daruruwan mayakan ISIL na ta kokarin ganin sun sami ikon wani yankin birnin Mosul a Iraqi, amma a jiya Alhamis kwamandojin Iraqi da jami’an Majalisar Dinkin Duniya sun ce dubban fararen hula sun makale a yankin, kuma suna cikin hatsari kasancewar fadan da ake yi.

Mayakan ISIL dai sun takurawa iyalai da ‘yan uwansu wajen shiga yakin da ake yi a Mosul, wanda yanzu haka ya zo karshe, sojojin Iraqi sunc e mayakan sun yi wa fararen hular barazanar kashe duk wani da ya yi kokarin guduwa daga yankin.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG