Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kai Wa Wasu Magoya Bayan ‘Yan Adawa Hari A Legas 


Dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar LP, Peter Obi (Hoto: Twitter/Peter Obi)
Dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar LP, Peter Obi (Hoto: Twitter/Peter Obi)

Dan takarar shugabancin Najeriya Peter Obi na jam'iyyar adawa ta Labour ya ce an kai wa magoya bayansa hari ranar Asabar inda aka raunata wasu gabanin wani gangamin yakin neman zabe da za a yi a birnin Legas, inda jam'iyya mai mulki ke da karfi sosai.

A zabukan da suka gabata a kasar da ta fi yawan jama'a a nahiyar Afirka, an yi fama da tashe-tashen hankula tsakanin magoya bayan jam'iyyun adawa, haka kuma an yi tashe-tashen hankulan siyasa da dama gabanin zaben 'yan majalisar dokoki da na shugaban kasa da za a yi ranar 25 ga watan Fabrairu.

"Ba za mu iya ci gaba da amincewa da hare-haren da ake kai wa 'yan adawar siyasa ba, wanda galibi ke kara ruruwa sakamakon kalaman tayar da hankali daga shugabannin siyasa," a cewar Obi a cikin wata sanarwa, inda ya bukaci 'yan sanda su gudanar da bincike.

Nan take dai ba a bayyana ko su wanene ke da alhakin kai harin ba, amma gidajen talabijin na kasar sun nuna motoci da dama da aka lalata dauke da allunan jam’iyyar Labour da kuma wasu magoya bayan jam'iyyar da suka jikkata ana musu jinya a wurin gangamin yakin neman zaben da aka gudanar a cikin garin Legas.

Nan take dai 'yan sandan yankin ba su ce komai ba.

A wajen gangamin, Obi ya shaida wa magoya bayansa cewa zai yi wa rundunar ‘yan sanda garambawul ta yadda zasu kara samun kwarewa, zai kuma kawo karshen satar man fetur da ke kawo cikas a harkar mai a yankin Naija Delta, da kuma inganta tsaro domin bai wa manoma damar bunkasa harkokinsu.

Obi ne ke kan gaba bisa ga wasu binciken jin ra'ayoyin jama'a, amma ana sa ran fafatwa a zaben zata yi zafi. Matasa masu kada kuri’a da suke jin takaicin yanayin tabarbarewar tattalin arziki, cin hanci da rashawa, da rashin aikin yi, su ne manyan masu goyon bayan Obi, a cewar kamfanin dillancin labaran Reuters.

Obi zai kara da Bola Tinubu, tsohon gwamnan jihar Legas kuma dan takarar jam’iyyar APC mai mulki, da kuma tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar na babbar jam’iyyar adawa ta PDP.

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG