Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kama Dan Sanda Farar Fata Da Ya Kashe Wani Baki Ya Janyo Zanga-Zanga a Amurka


George Floyd protesters set Minneapolis police station afire
George Floyd protesters set Minneapolis police station afire

An damke wani dan sanda farar fata da ya danne wuyar wani bakar fata da gwiwarsa, bayan kuma an buga ma bakar fatan ankwa a hannu a birnin Minneapolis na Amurka, wanda har ta kai ga bakar fatan ya mutu bayan da ya yi ta gaya masu cewa baya iya numfashi. An tuhumi dan sandan da laifin kisan kai.

Attoni-Janar din Karamar Hukumar Hennepin, Mike Freeman ya bayyana tuhumce-tuhumce jiya Jumma’a bayan da ya ce ofishinsa na da isassun shaidun tabbatar da wadannan tuhumce-tuhumcen. Nan take dai Freeman bai bayyana dalla-dallar tuhumce-tuhumcen ba to amma ya ce za a bayyana wata tuhumar aikata babban laifi daga bisani.

Wanda abin ya shafa, George Floyd dan shekaru 46 da haihuwa, an tabbatar da mutuwarsa jim kadan bayan da aka maka shi da kasa yayin da ankwa ke hannunsa, kuma dan sanda Derek Chauvin ya danne masa wuya da gwiwa yayin da Floyd ke cewa bai iya numfashi.

Iyalan marigayi Floyd dai sun mai da martani da cewa su na bukatar ,masu gabatar da kara su dada tsananta tuhumar.

Tuni wannan al’amari ya janyo zanga-zanga a wasu biranen Amurka ciki har da Washington, D.C. da gidan Shugaban Kasa na White House.

Facebook Forum

TASKAR VOA: Fim Da Aka Shirya Kan Leah Sharibu Ya Samu Lambar Yabo
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:26 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Kalubalen Da Masu Fama Da Lalurar Galhanga Ke Fuskanta
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:26 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Tasirin Cibiyar Kula Da Lafiyar Mata Da Yara Ta HopeXchange A Ghana
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:41 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hukumomi Sun Fara Shirin Bada Gudumawar Jini A Fadin Najeriya
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:54 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG