Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kama Mutum Bakwai a Sokoto Dake Da Hannu a Garkuwa Da Dan Kasar Amurka a Nijar


Dakarun Amurka dake nahiyar Afirka.
Dakarun Amurka dake nahiyar Afirka.

A ci gaba da bincike tare da bibiyar wadanda ake tuhuma da hannu a garkuwa da aka yi da wani dan kasar Amurka da aka sace a Jamhuriyar Nijar, wanda tuni sojin Amurka suka kubutar da shi a Najeriya, wani ayarin jami'an ‘yan sanda na musamman ya dira Sokoto, tare da damke wasu mutane kan batun.

Ayarin ‘yan sandan sun shiga Sokoto ne bayan bibiyar lambobin wayar da aka yi amfani da su, lokacin garkuwa da dan Amurkan, inda yanzu haka aka kama mutane bakwai a kauyen Dambar Dikko dake karamar hukumar Illela.

Sai dai mutanen da aka kama sun yi korafin cewa bayan da aka kama su, an nemi su biya kudaden beli domin a sake su. Lamarin da ya sa mutanen suka sanar da kungiyar kare yancin bil Adama ta Human Right Watch.

Da suke mayar da martani, ofishin ‘yan sanda na yanki na 10 mai kula da jihohin Sokoto da Kebbi da kuma Zamfara, ya ce yana sane da zuwan ayarin kuma sun yi aikinsu bisa ka’ida. Kakakin rundunar ‘yan sandan Bashir Musa, ya bayyana cewa kudaden da aka karba bana beli bane, an karbi kudaden ne kamar yadda aka saba a duk lokacin da za a ajiye wani da ake tuhuma, kuma an mayar musu da kudadensu.

Yanzu haka dai wasu daga cikin wadanda aka kaman tuni an wuce dasu Abuja, yayin da aka bayar da belin wasu wadanda bincike ya nuna basu da laifi.

Domin karin bayani saurari rahotan Muhammad Nasir.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:09 0:00


XS
SM
MD
LG