Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kama Tsohon Firayin Ministan Malaysia Najib Razak


Tsohon Firayin Ministan Malaysia Najib Razak

jami'an tsaro sun yi awon gaba da tsohon firayin ministan kasar Malaysia Najib Razak, wanda ake sa da aikata laifin wawurar kudin gidauniyar 1MDB da ya kirkiro lokacin da yake mulki.

.An kama tsohon Firai ministan kasar Malaysia Najib Razak dangane da wani abin fallasa na biliyoyin dala da ya shafi kudin gidauniyar raya kasa da ake kira 1MDB.

Majiyu sunce jami’an hukumar yaki da cin hanci da rashawa ne suka kama Najib ne a gidansa yau da safe.

Gobe Laraba ake kyautata zaton tuhumar tsohon Firai ministan. Ana zargin Najib da laifin wawurar kudin gidauniyar ta 1MDB da ya kirkiro lokacin da yake mulki. Ma’aikatar shari’a ta Amurka ta bayyana cewa, an wawure dala miliyan dubu hudu da dari biyar daga gidauniyar ta 1MDB, wadansu kudaden kuma sun karasa a bankunan ajiyar Najib.

Wannan abin fallasar ya janyo mummunan kaye da jam’iyar National Front Coaliation ta Najib ta sha, wadda ke mulkin kasar Malaysia tunda ta sami ‘yancin kai a shekarar alib da dari tara da hamsin da bakwai.
Najib ya musanta zargin

Facebook Forum

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG