Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kame Wata Yarinya ‘Yar kunar Bakin Wake Wadda Tace Tana Cikin Yan Matan Chibok.


Masu Zanga-Zanga sun bukaci Gwamnati dasu kubuto da 'yan matan Chibok da aka sace, 14 ga Oktoba 2014.
Masu Zanga-Zanga sun bukaci Gwamnati dasu kubuto da 'yan matan Chibok da aka sace, 14 ga Oktoba 2014.

Jamiaan tsaro a kasar Kamaru suna tsare da wasu yara ‘yan mata biyu wadda daya daga cikin su tace tana cikin ‘yan matan nan na chibok da boko haram ta sace a cikin shekarar 2014.

Mahmud Lalo ya tattauna da wakilin muryar Amurka Muhammadu Awal Garba kan wannan lamar. Ga kuma bayanin da yayi masa.

Karin bayanin dake ciki shine hakika an samu ‘yan mata 2 ne dake shekaru kasa da shekaru 15 wadanda suka zo wani gari da ake kira Limani a can jihar Arewa mai nisa wanda bakin iyakar tarayyar Najeriya da jamhuriyar Kamarwato kilomita 2 tsakanin su da Kamaru da Najeriya.

Wadannan ‘yan mata guda biyu daga cikin su ta bayani cewa tana daga cikin wadanda aka sace daga makarantar chibok kuma an same su da Boma-Bomai a jikin su, kafin su tayar boma-bamai din ne sai ‘yan kato da gora suka yi nasarar cafke su.

Ga Mahmud Lalo da ci gaban hirar 2’25

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:25 0:00

XS
SM
MD
LG