Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kammala Cinikin Sayar Da Chelsea Ta Ingila


'Yan wasan Chelsea

An kammala hada-hadar kasuwancin sayar da kungiyar kwallon kafar Chelsea ta Ingila, tsakanin mamallakin kungiyar mai barin gado, Roman Abromavic, da kuma hadakar kamfanoni a karkashin jagorancin hamsahkin attajiri dan kasar Amurka, Todd Boehly.

A yau Litinin aka rattaba hannun sauya shugabanci da mallakin kungiyar tare da amincewar dukan hukumomin da ke da ruwa da tsaki, ciki har da gwamnatin Birtaniya, wanda ya kai karshen zamanin Abromavic dan kasar Rasha, na tsawon shekaru 19 yana tafiyar da kungiyar.

Adadin kudin da aka yi cinikin kungiyar ya kama fam m.d.4 da m.250, inda kudin da aka sayi kungiyar ya kama fam m.2 da m.500, tare da yarjejeniyar rarar asusun tafiyar da kungiyar na tsawon shekaru fiye da 10, da ya kama fam m.1 da m.750.

Tun a watan Maris ne aka saka kungiyar ta Chelsea a kasuwa, sakamakon takunkumin da gwamnatin Birtaniya ta kakabawa Abromavic, bisa tuhumar dangantakarsa da shugaban Rasha Vladmir Putin, a mamayar da kasar ta Rasha ta kai wa Ukraine.

Hadakar kamfanonin na Boehly, sun yi takarar samun mallakar kungiyar ne da takwarorinsu 11, a fafutukar da aka soma tun a ranar 2 ga watan Maris.

A daya bangaren kuma rahotanni na tabbatar da yiwuwar komawar dan wasan tsakiya na Barcelona Ousmane Dembele zuwa kungiyar ta Chelsea a wannan bazara.

Wasu majiyoyi na bayyana cewa tuni da dan wasan dan kasar Faransa mai shekaru 25 ya amince da komawa kungiyar, inda zai kasance cefane na farko da sababbin mamallakan kungiyar za su yi bayan cimma daidaiton sayenta a yau Litinin.

Chelsea ta sami nasara akan kungiyar PSG ta kasar Faransa da ta nuna sha’awar dan wasan domin cike gibin Angel Di Maria, da kuma bukatar da Kylian Mbappe ya gabatar mata na sallamar Neymar da sayo Dembele, a yayin da take neman ya ci gaba da zama a kungiyar.

Ko bayan PSG ma, manyan kungiyoyi da dama suna zawarcin Dembele, wanda rahotanni suka bayyana cewa ya zabi ya sake hadewa da tsohon kocinsa Thomas Tuchel a Chelsea.

Dembele ya koma Barcelona ne a shekara ta 2017, inda ya sami zura mata kwallaye 32 a cikin wasanni 150, a yayin da kuma ya kwashe tsawon lokuta yana fama da rauni.

Kwantaraginsa na shirin kai wa karshe da Barcelona a ‘yan makwanni masu zuwa, a yayin da wasu majiyoyi suka bayyana cewa bai da ra’ayin wani sabon kwantaragi, wanda hakan zai saukaka komawarsa Chelsea.

A kasar Spain din kuma, shahararren dan wasan kungiyar Real Madrid Marcelo, ya tabbatar da cewa zai bar kungiyar a wannan bazara, bayan kwashe tsawon shekaru 15 yana taka leda a kungiyar.

Marcelo dan kasar Brazil ya koma Barcelonar ne tun a shekara ta 2007, inda ya sami nasarar lashe kofunan gasanni har 25, kuma yanzu haka yana rike da mukamin kaftin din ‘yan wasan kungiyar.

Saurari rahoton Murtala Sanyinna:

please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:02:53 0:00

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG