Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kara Farashin Man Diesel A Jamhuriyar Nijar


Karancin man fetur.
Karancin man fetur.

Gwamnatin jamhuriyar Nijar ta bada sanarwar kara kudin man diesel a gidajen man kasar sakamakon dalilan da ta kira masu nasaba da yakin Ukraine.

Wannan matakin dai tuni ya fara shan suka daga wasu ‘yan kasar saboda a cewarsu abu ne da ka iya kara tsunduma jama’a cikin halin kuncin rayuwa.

Da yake bayani dangane da wannan mataki lokacin da ya bayyana a kafar gwamnatin Nijar Ministan kasuwanci, Alkache Alhada, ya ce daga ranar Litinin 1 ga watan Agusta, farashin litar Gazoil ko kuma man diesel ya tashi daga dala dari da dala 7 da tamma 1 na cfa (538 fcfa) zuwa dala dari da talatin da uku da tamma 1 (668 fcfa).

Wannan na nufin an sami karin dala ashirin da shidda (130 fcfa) a kowane litar. Matakin ya biyo bayan karancin man diezel din da yakin Ukraine ya haddasa a kasashen duniya in ji ministan.

Sai dai wani dan rajin kare hakkin dan adam bugo da kari tsohon shugaban gidan mai na Mobile, Alhaji Salissou Amadou, ya ce bai gamsu da wannan hujja ba.

Ya ce wannan wani salo ne na yaudara da cuta, amma cewa yakin Ukriane ya sa a kara kudin man bai taso ba.

Jamhuriyar Nijar wacce ke hako ganguna 20,000 a kowace rana kan ware ganguna 7000 na tataccen man domin amfanin cikin gida yayin da akan sayar da ganguna 13,000 ga kasashe makwabta irinsu Najeriya, Mali, Burkina Faso, Togo, Benin da kuma Ghana.

Amma yanayin karanci da tsadar man diesel din da aka shiga a wadannan kasashe a washegarin mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine ya tilasata wa direbobi da dama ketarowa Nijar domin cika tankunan motocinsu, lamarin da ke haddasa dogayen layuka a gidajen mai saboda haka hukumomi suka yanke shawarar kara kudin Gazoil kwatankwacin yadda abin yake a ko ina a nahiyar Afirka, in ji ministan.

Ganin irin alakar da ke tsakanin sha’anin sufuri da man fetur da kuma irin yadda abin ke tasiri akan sha’anin kasuwanci ya sa magidanta irinsu Malam Halidou soma nuna damuwa akan yiyuwar fuskantar hauhawar farashin abinci sanadiyar matakin gwamnatin.

Ministan kasuwanci Alkache Alhada ya nanata cewa karin farashin bai shafi man fetur da kalanzir ba, ya kuma yi tunatar wa akan cewar a bisa ka’ida a kowane wata gwamnati kan sake duba farashin da ya cancanta a sayar da man dai-dai da yanayin da ake ciki a kasuwannin duniya.

Da ma dai tun a makonnin baya aka fara yada jita jitar cewa, wasu mukarraban gwamnatin Nijar sun fara yunkurin aiwatar da karin kudaden man fetur, sai dai a wancan lokaci shugaban kasa bai yi na’am da wannan shawara ba.

Saurari cikakken rahoton Souley Moumouni Barma:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:07 0:00

XS
SM
MD
LG