Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kara Kashe Wasu Falesdinawa 7 A Bakin Iyakar Gaza Da Izraila


Falesdinawa 7 ne sukarasa ransu a wani taho mu gama da sukayi da sojojin Israela dake bakin iyakar Gaza da Israela.

Ma’aikatan kiwon lafiya na Falesdinu sunce sojojin Israela sun kashe Falesdinawa 7 a jiya jumaa lokacin da dubban su suka taru a bakin iyakar Isreala da Gaza.

Maaikatar kiwon lafiya ta kasar Faledinu tace cikin wadanda akakashen ko har da wani dan shekaru 16, kuma rahotanni sun bayyana cewa falesdinawa 408 ne aka jima rauni sakamakon wannan rikicin.

Wannan dai shi ya kawo adadin Falesdinawa 27 kenan aka kashe tun daga makan jiya lokacin da aka fara wannan zanga-zangar.

A jiya juma’a dai lokacin zanga-zangar sojojin Israela sun harba hayakin nan maisa kwalla, kana suka yi harbi da harsashin roba harma da harsashi na kwarai domin ganin masu zanga-zangar basu samu nasarar balle shingen bakin iyakar ba.

Domin ko masu zanga-zangar sun kona taya kusa da bakin iyakar, wanda wannan yasa hayaki ya tirnuke sama daf da bakin shingen dake bakin iyakar.

Sojojn Israela suka ce masu zanga-zangar sun ta jefar su da wasu abubuwan fashewa, yayin da wasun su ma sunyi kokarin tsallake shingen bakin iyakar.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG