Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kara Kudin Ruwa Daga Kaso 18.75  Zuwa 22.75 A Najeriya


Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Yemi Cardoso
Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Yemi Cardoso

Kwamitin tsare-tsaren tsaren manufofin kudin babban Bankin Najeriya wato MPC na CBN ya kara kudin ruwa da maki dari hudu daga kaso 18 da digo 75 zuwa kaso 22 da digo 75.

Gwamnan babban bankin CBN, Yemi Cardoso ne ya bayyana hakan jim kadan bayan taron kwamitin manufofin bankin wato MPC na farko a bana a birnin tarayyar kasar, Abuja a yau Talata.

Baya ga batun kudin ruwa da aka kara, daraktan sashen kula da manufofin kudin bankin CBN, Malam Muhammad Musa Tumala, ya ce za’a hukunta duk wani bankin kasuwanci na kasar da aka kama da laifin boye dala ko yiwa kokarin gwamnati na kawo sauki ga wahalar da al’umma ke ciki a halin yanzu.

A cewar Cardoso, dukkan mambobin kwamitin MPC 12 sun yanke shawarar kara tsaurara manufofin kudi ta hanyar kara maki 400 kan kudin ruwa wanda ya kai shi kaso 22 da digo 75 daga kashi 18 da digo 75 cikin 100.

Mambobin Kwamitin Manufofin Kudin CBN
Mambobin Kwamitin Manufofin Kudin CBN

Kwamitin ya kuma daidaita tsarin bangaren ''asymmetric'' na manufofin kudin a maki +100 zuwa -700 daga yadda yake a da na maki 100 zuwa -300," in ji Cardoso.

Idan Ana iya tunawa kudin ruwan ya kasance a kan kaso 18 da digo 75 tun daga taron kwamitin MPC na ƙarshe tsakanin ranar 24 zuwa 25 na watan Yulin shekarar 2023.

Haka kuma Cardoso ya kara da cewa ganin irin hauhawar farashi dake kan kaso 29 da digo 90 a halin yanzu, sabon kudin ruwan da aka daga makinsa na daga cikin matakan da gwamnati ke dauka na magance hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya inda aka daga darajar kudadden ajiyar ''Cash Reserve Ratio'' wato CRR zuwa kaso 45 a yayin da ba’a taba adadin kudin dake yawo a cikin kasar na kaso 30 cikin 100 ba wato ''liquidity ratio'' a turance.

Gwamnan CBN ya kuma ce a cikin shekaru 4 da suka gabata sama da dala biliyan 26 sun bi hada-hada ta hanyar manhajar krifto wato Binance Nigeria.

Wannan dai shi ne karon farko da aka gudanar da taron kwamitin manufofin kudi na bankin CBN tun bayan nada gwamna Yemi Cardoso a matsayin jagoran bankin.

A saurari rahoton Halima Abdulrauf:

An Kara Kudin Ruwa Daga Kaso 18.75  Zuwa 22.75 A Najeriya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:08 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG