Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Karfafa Matakan Tsaro A Jahar Filato Domin Bukin Kirsimeti


Jami'an tsaro

Rundunar tsaro a jahar Filato tace ta ‘dauki matakan tabbatar da gudanar da bukukuwan Kirsimeti da na sabuwar shekara lafiya.

Kwamandan rundunar wanzar da zaman lafiya a jahar Filato Manjo Janar Rogers Nicolas, yace rundunar ta ‘kara shingaye don gunadar da binciken abubuwan hawa musamman a yankunan dake da barazanar tsaro a cikin birnin Jos da kan iyakar jahohin dake kewaye da jahar Filato.

Rundunar tsaron dai ta yi kira ga al’ummar jahar da idan har suka ga wani abin da bai dace ba da ayi sauri a tuntubesu domin ‘daukar matakan gaggawa.

Wakiliyar Muryar Amurka, Zainab Babaji, ta leka kasuwa idan mabiya addinin Krista ke hada-hadar sayan kayayyakin bikin Kirsimeti, inda kuma taci karo da Madam Theresa Gofen, wadda tace a baya takan sayawa yaro ‘daya kayayyakin sawa uku amma yanzu tace da kyar in zata iya sayan biyu saboda tashin farashin kayan.

Sai dai ita kuma Madam Ester, na ganin farashin kayayyakin sawa basu tashi kamar yadda ake gani ba, amma farashin kayan abinci ya tashi.

Domin karin bayani saurari rahotan Zainab Babaji.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:21 0:00

XS
SM
MD
LG