Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kasa Cimma Matsaya a Tattaunawar Sudan Ta Kudu


Daga hagu ga Riek Machar, daga dama kuma Salva Kiir

Kamar yadda wasu da dama su ka nuna fargaba, an kasa cimma jituwa a tattaunawar da aka yi tsakanin Shugaban Sudan Ta Kudu da jagoran 'yan tawaye, Riek Machar.

An kammala tattaunawa tsakanin Shugaban Sudan Ta Kudu Salva Kiir da jagoran 'yan tawaye Riek Machar a birnin Addis Ababa na kasar Habasha ba tare da cimma wata yarjajjeniya ba, to amma watakila mutanen biyu za su sake ganawa, mai yiwuwa ma nan da sati biyu a birnin Khartoum na kasar Sudan.

Ministan Yada Labaran Sudan Ta Kudu Michael Makuei, wanda ya dawo Juba daga Addis Ababa jiya Jumma'a, ya gaya ma manema labarai cewa Majalisar Ministocin kungiyar kasashen kuryar Afirka, IGAD a takaice; sun ayyana kawo karshen ganawar ta Addis Ababa.

Ya ce Shugabannin kungiyar ta IGAD sun yi kira ga Kiir da Machar da su cigaba da tattaunawa kan batutuwan da har yanzu su ke da sabani; su kuma amince su gana a Khartoum babban birnin kasar Sudan a sati mai zuwa, sannan in ta yiwu, a yi taro na gaba kuma a birnin Nairobin Kenya.

Wakilan Kiir da Machar duk su ma sun tabbatar cewa ba a cimma jituwa a ganawar ta Addis Ababa ba.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG