Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kashe Akalla Mutane 74 Ciki Harda 'Yan Jarida Biyu A Syria.


Jakadan Syria a majalisar dinkin duniya yake jawabi ga babban zaurenta
Jakadan Syria a majalisar dinkin duniya yake jawabi ga babban zaurenta

Akalla mutane 74 ne ake zargin dakarun Syria suka kashe ciki har da ‘yan jarida daga kasashen yammacin duniya biyu a fadin kasar a wunin jiya laraba.

Akalla mutane 74 ne ake zargin dakarun Syria suka kashe ciki har da ‘yan jarida daga kasashen yammacin duniya biyu a fadin kasar a wunin jiya laraba, musamman a birnin Homs babbar tungar ‘yan hamayya, sakamakon barin bam babu kakkautawa da dakarun suka yi.

Gwamnatin Faransa ta bayyana ‘yan jarida biyu da aka kashe a Homs, da cewa sune Marie Colvin, ba Amurkiya fitacciyar wakili a fagen daga dake aiki da jaridar Sunday Times ta Ingila da kuma wani dan Faransa mai daukan hotuna Remi Ochlik.

‘Yan gwagwarmaya sunce ‘yan jarida masu yawa dake aiki a wata cibiyar ‘yan jarida ta wucin gadi sun jikkata a gundumar Baba Amr dake hanun ‘yan tawaye, kuma suka ce da gangan aka auna hari kan cibiyar.

PM Ingila David Cameron yayi ta’ziyya da jinjinawa ga Colvin.

Gwamnatin Syria ta bada sanarwa wacce a ciki tace bata da labarin cewa ‘yan jaridan suna cikin kasar. Daga nan tayi kira ga duk wani mai neman labarai dake cikin kasar ba bisa ka’ida ba ya dauki matakin dai-daiata zamansa cikin kasar.

XS
SM
MD
LG