Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kashe Dakarun Majalisar Dinkin Duniya Hudu a Mali


Wasu dakarun Mali yayin da suke atisaye
Wasu dakarun Mali yayin da suke atisaye

Mako guda bayan kisan da aka yi wa wasu dakarun kasar Mali, an kashe sojojin wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya hudu a yankin Mpoti.

Majalisar Dinkin Duniya, ta ce an kashe dakarunta da ke wanzar da zaman lafiya a jiya Laraba, yayin da motarsu ta taka nakiya a tsakiyar kasar Mali.

Rundunar wanzar da zaman lafiya a kasar ta Mali da aka fi sani da MINUSMA, ta ce dakarun na tafiya ne a tsakanin Boni da Dountza a yankin da ake kira Mpoti.

Baya ga wadanda suka mutu, wasu dakarun hudu sun samu munanan raunuka a cewar rundunar.

A ranar Talatar da ta gabata aka kashe wasu dakarun Mali shida a wannan yanki, a wani lamari mai kama da wannan.

Kakakin Majalisar Dinkin Duniya, Stephane Dujarric, ya ce, Sakatare Janar, Antonio Guterres, ya yi Allah wadai da wadannan hare-hare da aka kai akan dakarun.

Ya kuma ce, wannan hari, wanda ya kwatanta a matsayin na “ragwanci” ba zai kashe wa rundunar ta MINUSMA kwarin gwiwa ba, a yunkurin da ta ke yi na ganin mutanen Mali sun samu zaman lafiyan da suke muradi.

A shekarar 2013 aka tura dakarun na Majalisar Dinkin Duniya su 11,000 zuwa Mali, domin yakar masu tsatsauran kishin addini da kuma tabbatar da doka da oda.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG