Rundunar Sojin Amurka da ke Afirka AFRICOM, ta ce wasu hare-haren jiragen sama da suka auna kungiyar mayakan Al-Shabab da ke Somalia ya yi sanadin mutuwar farar hula biyu baya ga raunata wasu guda uku.
Gano hakan ya biyo bayan binciken da aka yi, wanda aka saka sakamakonsa a rahoton kwatan farko na AFRICOM, game da fararen hular da aka rutsa da su.
Kuma shi ne karo na biyu a tarihin rundunar, da ta ce fararen sun mutu a Somaliya sanadiyyar harin jiragen sama da Amurka ta kai kan mayakan masu tsaurin ra’ayin addini.
A dai watan Fabrairun da ya gabata aka wadannan hare-haren.
“Tun bayan da na fara jan ragamar wannan runduna, mun dada mai da hankali kan bayyana gaskiya game da harkokin da mu ke gudanarwa,” a cewar Janar Stephen Townsend, Kwamandan AFRICOM.
Townsend ya bayyana hakan ne a wata takardar bayani da aka raba ma manema labarai a jiya Litinin.
Ya kara da cewa, “Idan mun gaza, za mu fito fili mu amsa cewa mun gaza.”
Kwamandan ya ce an kashe farar hulan cikin abin da ya kira, “yanayi na takaici da kuskure” a harin na ranar 23 ga watan Fabrairun 2019.
Harin ya kuma yi sanadin mutuwar wasu ‘yan ta’addar al-Shabab biyu, wadanda da ma su aka auna.
Za ku iya son wannan ma
-
Fabrairu 26, 2021
Gwamnatin Nijar Ta Mayar Da Martani Game Da Tarzomar Zabe
-
Fabrairu 25, 2021
An Kama Masu Zanga Zanga Sama Da 200 a Nijar
-
Fabrairu 25, 2021
Ghana Ta Sami Kason Farko Na Rigakafin Coronavirus
-
Fabrairu 23, 2021
NIJAR: Bazoum Mohamed Ya Lashe Zaben Shugaban Kasa
-
Fabrairu 23, 2021
Wai Ko Wa Ake Ganin Zai Lashe Zaben Shugaban Kasa A Nijar?
-
Fabrairu 22, 2021
Ana Jimamin Mutuwar Jami'an Zabe Bakwai Da Suka Rasu a Nijar
Facebook Forum