Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An kashe jakadiyar kasar Venezuela a Kenya


Shugaban kasar Venezuela Hugo Chavez

‘Yan sandan kasar Kenya sun ce an gano gawar jakadiyar kasar Venezuela ta wucin gadi a kasar Kenya a gidanta dake birnin Nairobi

‘Yan sandan kasar Kenya sun ce an gano gawar jakadiyar kasar Venezuela ta wucin gadi a kasar Kenya a gidanta dake birnin Nairobi, wadda ta mutu bayan an makare ta.

Jiya jumm’a, babban jami’in ‘yan sandan kasar Kenya ya bayyana sunan jakadiyar a matsayin Olga Fonseca Gimenez, babbar jami’ar ofishin jakadanci kuma mai rikon mukamin jakadiyar kasar Venezuela a Kenya.

Jami’an kasar Kenya sun ce Fonseca ta isa birnin Nairobi ne ranar 15 ga watan Yuli ta maye gurbin jakade Gerardo Carillo-Silva.

Kamfanin dillancin labarai- Associated Press, ya laburta cewa, Carillo-Silva ya bar kasar Kenya bayanda wadansu ma’aikata maza uku a ofishin jakadancin suka rubuta takarda suna korafin cewa, yana matsa masu da neman yin lalata. Rahoton ya bayyana cewa, Fonseca ta yi barazanar korar ma’aikatan idan basu janye wasikar korafin ba.

Yan sanda suna gudanar da bincike kan kisan Fonseca. Kawo yanzu basu bayyana dalilin kashe ta ba.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG