Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kashe Kimanin Mutane 13 A Wani Hari Da Aka Kai Garin Ibbi.


Mutane suka hallara a wurin da aka kai harin kunar bakin wake a jalingo, a jihar Taraba.

Kimanin mutane 13 suka rasa rayukansu a wadansu hare hare da aka kai a garin Ibbi jihar Taraba, fiye da ashirin kuma suka jikkata

Wasu mahara dauke da muggan makamai sun kai sababbin hare-hare a wadansu yankunan karamar hukumar Ibi,dake makwabtaka da jihar Filato,a jihar Taraba.

Wakilin Sashen Hausa Ibrahim Abdul’Aziz ya ruwaito cewa, kimanin mutane 13 suka rasa rayukansu a hare haren, fiye da ashirin kuma suka jikkata.

Jami'an tsaro sun bayyana cewa tuni aka tura karin jami’an tsaro domin maido da doka da oda.

Wannan lamarin dai ya sa mazauna yankin Ibi tsirawa kabilar Tarok hannu da kai hare haren, zarginda al’umar ta musanta.

Ga ci gaban rahoton.

Hari a Ibbi, Jihar Taraba
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:34 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG