Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kashe Kimanin Mutane Hamsin a Wasu Kauyukan Jihar Zamfara


Mazauna kauyukan Tungar Kafau, da Mallamawa, da Shinkafi da wasu kauyuka a jihar Zamfarar Najeriya suna cikin zaman fargaba sakamakon wasu hare haren da wasu yan ta’adda suka kai musu tsakanin kwanaki biyu, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane kusan hamsin a wadannan kauyukan a Zamfara.

Rahotanni daga shedun gani da ido sun ce an kashe mata ashirin da shida a kauyen Tungar Kafau kana aka kashe maza goma sha tara a wani samame da wasu yan ta’adda da ake zaton barayin shanu ne da suka saba kaiwa mutane yankin hare hare.

Dr. Suleiman Shuaibu na kungiyar Amnesty International dan asalin wannan yanki ne, yace ya zuwa yanzu babu wani jami’in tsaro da ya kawo dauki ga mutanen yankin. Ya kara da cewar mutane wannan yankin sun dade suna fama da hare haren barayin shanu kuma hukumomi sun nade hannu babu wani takamaiman mataki da suke dauka na gani kawo karshen wannan lamari.

Mutanen yankin sun yi kira ga gwamnatin tarayya da ta jiha da su gaggauata daukar matakin kawo karshen abinda suka kira kisar kiyashi da barayin shanu ke musu. Sun ce rashin daukar matakin hukuma zai tilasta musu dauakr matakan kare kansu.

please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:03:03 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG