Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kashe Kwamandan Wata Kungiya Mai Alaka da ISIS


Janar John Nicholson kwamandan sojojin Amurka dake Afghanistan
Janar John Nicholson kwamandan sojojin Amurka dake Afghanistan

Rahotanni sun bayyana cewa an kashe Wani babban kwamandan kungiyar Khorasa, wadda reshe ce ga kungiyar ISIS, wadda kuma aka ce tana da hannu dumu-dumu a cikin jerin hare-haren kunar bakin wake da wasu munanan ayyuka.

An dai kashe kwamandan ne a wani martanin harin ta’adanci da aka kai a gabashin Afghanistan, kamar yadda jami’an Amurka da na Afghanistan din suka ruwaito jiya Alhamis.

Shi dai wannan kwamanda mai suna Qari Munib, an kashe shi ne a wata arangama da a kayi inda dakarun Afghanistan da taimakon sojojin Amurka suka kai a gabashin Afghanistan din da niyyar murkushe ayyukan ta’addanci a yankin.

Kamar yadda sanarwar da ta fito daga ma’aikatar tsaron Amurka ta Petagon ke cewa a jiya Alhamis, wannan harin ya faru ne a ranar tara ga wannan watan a gundumar Achin dake Lardin Nangarhar.

Sanarwar da Pentagon ta fitar ga ofishin shugaba Ashraf Ghani, ta bayyana cewa Munib shine kanwa uwar gami na tagwayen hare-haren da aka kai a Kabul da kuma wasu ayyukan assha da aka gudanar a gundumar Achin na Lardin na Naganhar wanda ke bakin iyaka da kasar Pakistan.

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG